Yanzu Haka Yan Sanda suna Harbe harbe a wajen da aka ajiye Abincin tallafin Corona a abuja

Yanzu haka jami’an tsaro suna harbi kan mai uwa da wabi a daidai UTC din da ke Area 10 a Abuja yayin da wasu ‘yan daba suka yi kokarin kutsawa cikin ginin fasaha da al’adu inda ake zargin ana ajiye kayan agaji na COVID-19. Jami’an tsaron da suka hada da ‘yan sanda, sojoji, ma’aikatan DSS sun fatattaki wadannan bata gari wadanda burinsu shi ne wofantar da wurin. An yi harbe-harbe da yawa cikin iska a kokarin tarwatsa ‘yan da bar Har zuwa lokacin wannan rahoton, yankin, wanda aka fi sani da cibiyar kasuwanci ya kasance babu kowa a ciki yayin da jami’an tsaro suka kewaye ginin.

Lamarin da ya haifar da hayaniya yayin da ‘yan kasuwa da masu wucewa ke yin sumame don kare lafiya. An samu rahotanni da dama na wawure kayan tallafi na COVID-19 a yawancin jihohin kasar da wasu ‘yan daba suka yi bayan fitinar da ta faru sakamakon kisan masu zanga-zangar lumana a yankin Lekki Toll Gate da ke Legas da Sojojin Najeriya suka yi a daren Talata. Masu zanga-zangar da aka kashe suna neman a kawo karshen zaluncin ‘yan sanda da danniyar jihar lokacin da sojoji suka katse rayukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.