‘Yar Gwamna Ta Kamu Da Covi-19.

Gwamnan jihar Ebonyi, Cif David Umahi ya ce ‘Yarsa da wasu mutane uku na kusa dashi sun kamu da cutar COVID-19.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Barr. Uchenna Orji, ya fitar wadda aka tura zuwa DAILY POST a Abakaliki, ya tabbatar da sakamakon.

A cewar sa: “Gwamnan Ya bayyana cewa ‘yarsa da wasu na kusa da shi ma sun yi gwajin Covi-19 kuma sakamakonsu ya nuna suna dauke da kwayar cutar”.

Gwamnan ya yi godiya ga Allah saboda alherinsa da ikon warkarwa kuma ya godewa jama’ar jihar Ebonyi da Najeriya saboda addu’o’in su da hadin kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.