Labarai

Lallai Buhari ka Kori shugabanin Jami’an tsaro ~Shekarau ga Buhari

Spread the love

Sanata Ibrahim Shekarau a ranar Alhamis din da ta gabata ya yi nuni da cewa shugabannin tsaron za su iya yin aiki fiye da kima, yana mai bayanin dalilin da ya sa za a sauke su daga aikinsu.

Kiraye-kiraye masu tsanani na cire su sun biyo bayan kalubalen rashin tsaro a fadin kasar.

Majalisar dattijai ta bukaci fadar shugaban kasa da ta sauya shugabannin hafsoshin a karo na biyu, bayan kisan baya-bayan nan da aka yi wa manoman shinkafa da dama a Zabaramari, jihar Borno.
Tsohon ministan ilimi kuma gwamnan jihar Kano har sau biyu, a gidan talabijin na Channels TV Sunrise Daily, shima ya bayyana gazawar Shugabannin tsaron

“Sojoji suna karkashin tsarin ne Akwai ka’idoji lokacin barin – ko dai ka kai shekaru 60 ko kuma ka yi aiki na tsawon shekaru 35, “in ji shi.
Amma Babban hafsan hafsoshin tsaron yanzu sun kai shekaru 39 suna aiki Duk banda babban hafsan tsaro wanda yake 58, duk sun fi 60.

“shekerun Babban hafsan hafsoshin ya sanya 37, shugaban hafsan sojin ruwa ya sanya shekaru 41.

“Abin da muke cewa shi ne koda Shugaban kasa ya same su da muhimmanci, a ba su damar yin ritaya kamar yadda suke yi a aikin gwamnati, kamar yadda doka ta tanada, kuma za ka iya daukar su a matsayin ministan tsaro, mai ba da shawara a kan tsaro, NSA, komai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button