Lokaci Ya Wuce Da Za’a Rufe Kofa Dani Don Yiwa Wani Zagon ‘Kasa A Siyasa, Bana Rigima Da Kowa, Bani Da Abokin Fada~Shekarau.
Sanatan Kano ta tsakiya malam Ibrahim Shekarau, yace shi baza’a rufe kofa dashi ba don ayiwa wani zagon ‘kasa ko don shirya wa wani tuggu ” bani da hujjar rigima da wani, na haura shekara 60 A rayuwar duniya, Allah ya rufamin asiri, duk Abinda nake nema Allah yabani, banga dalilin da zanyi rigima da wani ba Ko da wani Yana rigima dani toh ni be dameni ba”
Malam shekarau Yana wannan jawabi ne A yayin da yakarbi bakonci shugaban kwamtin ‘koli na siyasar Gidansa Dakta Umar Mustapha Mai Mansileta A Gidansa dake mundubuwa yayin wata ziyara ta musamman da suka kaimasa.
Ana zargin Ana samun takun saka tsakanin Gidan siyasar Gandujiyya da mabiya malam Ibrahim shekarau. Inda ya karyata batun da cewa labarin kanzon kurege ne.
Daga Abdulrashid Abdullahi Kano