Lokaci Ya Yi Da Yakamata Buhari Yayi Sulhu Da ‘Yan Boko Haram~ Majalisar Dinkin Duniya.
Matsalar Tsaro:- Majalisar Dinkin Duniya ta Shawarci Buhari kan Boko Haram.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Birnin Tarayya Najeriya Abuja, Ta Shawarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kan Matsalar Boko Haram da yakici yaki cinyewa sama da Shekaru Goma a Arewa Maso Gabashin Kasar Nan.
Sakataren Kungiyar ne ya Shawarci Buhari, Inda yace “Lokaci yayi da Yakamata Gwamnatin Buhari tayi Sulhu da ‘Yan Boko Haram.
“Yace Buhari yayi sulhu da Boko Haram tunda An kasa Cimma Nasara da Baking Wuta, Yakara da cewa an dauki makin Kawar da Boko Haram da karfin Soji Har Tsawon Shekaru 11 amma an kasa Cimma Nasara.
Yace “Wannan Matakin Na Sulhu Shi zai Taimaka a Cimma Nasara Inji Shi.
Masu karatu Ya dace Gwamnati tayi Sulhu da Su kodai a barsu da Sojoji…?
Ahmed T. Adam Bagas