Lokaci Ya Yi Da Za Ka Bayyana Mana Kishinka Ga Addinin Musulunci Ta Hanyar Saka Hannu A Takardar Hukuncin Kisan Da Aka Yankewa Matashin Da Yayi Batanci Ga Ma’aiki, Sakon Alkanawi Ga Ganduje.
Wani Matashin Dan Jarida a jihar Kano Sabiu Danmudi Alkanawi ya yi kira ga gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ya bayyanawa al’umma kishin da yake yiwa Addinin Musulunci ta hanyar rattaba hannu a takardar hukuncin kisan da aka yankewa mawakin da yayi kalaman batanci ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (s.a.w).
Alkanawi ya ce ba karamin abin takaici bane arika samun wasu jahilai dakikai kafirai suna yin kalamai na cin mutunci ga manzon Allah a cikin garin Kano wanda yake shine Cibiyar Masoya Manzon Allah (s.a.w) ta Afika baki daya.
Sabiu Danmudi Alkanawi ya kara da cewa shi hukuncin taba janibin Manzon Allah (s.a.w) nan take ake aiwatar dashi, ba a jinkirin yinsa ko kadan.
Alkanawi ya ce Babban abin da gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai yi wanda zamu tabbatar da yana kishin Addinin Musulunci shine ya gaggauta saka hannu a takardar hukuncin kisan da aka yankewa Matashin.
Da yake maida martani akan kiraye-kirayen da wasu kungiyoyi da mutane suke yi na asaki mai laifin, Alkanawi ya ce Jihar Kano jiha ce ta Musulmai, jiha ce wadda take da dokoki da Kotuna na Addinin Musulunci, kuma kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowacce jiha damar shimfida dokokinta yadda take so, dan haka babu dalilin da zai sa wasu ‘yan iska suzo suyi mana katsalandan a cikin al’amuran gudanarwar jiharmu, inji Alkanawi.