Labarai

Lokaci yayi da zamu kirkiri Ma’aikatar kula da fulani da kiwon shanu ~Inji Malami

Spread the love

Babban Attorney General kuma Babban Ministan shari’ah na Nigeria Abubakar Malami (SAN) ya bada shawara wa Gwamnatin Nigeria da ta kirkiri ma’aikatar kula da fulani makiyaya

Ministan yace rikici tsakanin fulani makiyaya da manoma yayi kamari matuka, akwai bukatar a dauki matakin gaggawa kafin ya haifar da matsala da zai shafi kasa gabaki daya

Kasar Nigeria da taswirar ta a duniya yankine na albarkatun noma, fulani suna mamayar kowani yanki na Nigeria don kiwon shanu, lokaci yayi da Gwamnati ya kamata ta kirkiri sabuwar hukuma da zata duba lamarin fulani makiyaya wanda hakan zai amfani kasa da ‘yan Nigeria

Malami ya tabbatar da cewa Nigeria zata zauna lafiya ne idan aka bi doka, sannan aka kiyaye ‘yancin ‘dan kasa wanda ya hada da, ‘yancin zama a duk inda ‘dan Nigeria ya ga dama domin samar da zaman lafiya mai dorewa

Rikicin fulani da manoma gaskiya ne yana faruwa, akwai wadanda suke fakewa da rikicin suna haddasa fitina a cikin kasa, don haka akwai bukatar samar da ma’aikata da zata kula da wannan saboda a samu mafita

Sannan Ministan ya bada shawaran a ware yanki a ko’ina cikin Nigeria wa fulani makiyaya don suyi kiwon shanu, da kuma gina burtsatsen ruwa a gurare masu muhimmanci da ake kiwon shanu, tare da kafa asibitin kula da lafiyar dabbobi, da kuma kafa babbar kasuwar shanu inda mutanen kudu da Arewa zasu hadu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button