Labarai

Limamin Waje Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Spread the love

Limanin waje ya rigamu zuwa gidan gaskiya.

Wato Sheikh Nasir Muhammad Nasir ( inkiya Wazirin Kano Murabus)

Za’ai jana’iza gobe da misalin karfe 9 na safe.

Hoto: Sheikh Nasir Muhammad Nasir

Haƙiƙa duniya ba wajen zama bane, kamar yadda Hausawa ke cewa, komai nisan gona da akwai kunyar ƙarshe.

Mutuwa bata ƙyale wani domin wani, kuma takan ɗauki kowa idan lokacin shi yayi.

A irin wannan ɗaukan da take ne, ta ɗauki Sheikh Nasir Muhammad Nasir (Wazirin Kano Murabus) inkiya Limamin waje.

Allah yayi wa shahararren malamin rasuwa a wannan yammaci.

Rahotanni na nuna cewa, za’ai jana’izar sane da misalin karfe 9 na safe gobe a ƙofar kudu gidan sarkin Kano.

Yan Najeriya Sun Bayanna Ra’ayin su Game da Mutuwar

Lawan Sani Ibrahim Cewa yayi:

“Allahu Akbar Allah ya gafarta Masa kurakuransa yasa jannatul firdausi ce mako marsa“.

Rabiu Bala Tahir innalillahi yayi, tare da masa addu’a kamar haka:

Innalillahi waina illaihi rajiun. Allah ya ji kansa ya kai haske Kabarinsa. Allah ya sada shi da Annabi muhammadu S.A.W”.

Ibrahim Yusuf Bayero shima addu’a yayi ta hanyar faɗin:

Allah ya jikan shi da rahama yasa aljannah makona gare Shi“.

Hassan Ibrahim shima yayi addu’a ga mamacin:

Allah ya gafarta masa kuskurensa yasa kabarinsa dausayi ne daga gidan aljanna Allah ya kyautata namu zuwan”.

Fatan Allah ya kai rahama kabarin sa, yasa aljanna makoma ga musulmi baki ɗaya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button