A daidai lokacin da muke kukan satar mutane da fasakorin su, a lokacin zauren Majalisa ke baiwa wani jami’i lambar yabo da sunan jagoran hana satar mutane.
Amma domin wani dan sanda ya dauki kamera-man ya shiga jeji yana shirya film festival, su kuma su dauko shi suna bashi trophy kamar gwalo ne suke mana.
Maimakon bashi wannan lambar yabo kamata yayi su aika shi Zamfara, Katsina da Sokoto ya tabbatar sai an gama da masu satar mutane, sannan in ya dawo sai su bashi rabin Asokoro in sun ga dama.