Labarai

Ma’aikan Gwamnati Sun yiwa Gwamna Al’qunut kan rage musu albashi a jihar Neja.

Spread the love

A jiya Alhamis ne ma’aikatan Gwamnatin a Jihar Neja, suka yi Sallah raka’a 2 a Masallatan Idi, kana sukayi Addu’ar Allah ya Kwatar musu hakkinsu a Wajen Gwamnatin Jihar domin ta zaftare musu albashi kaso 30% Na kowanne ma’aikaci Inji Su.

Wannan al’qunut anyi a Minna babban birnin Jihar, Anyi a Masallacin Idin Kura karamar hukumar Shiroro, da Agaie da sauran kananan Hukumomi a Fadin Jihar.

Sai dai da farko ma’aikatan sun sanar cewa zasuyi addu’ar ne akan Matsalar Tsaro, amma da Suka Isa wurin sai suka buge da yiwa Gwamnati al’qunut.

Jaridar Mikiya ta samu zantawa da wasu mutane 2 da sukace a sakaya sunansu cikin wadanda suka yi al’qunut din a minna, sai sukace Idan sun sanar cewa zasuyi al’qunut ne kan hakkinsu da gwamnati ta Tauye, za’a Iya hanasu, shi yasa sukace addu’a zasu yiwa Jihar, yace “duk da haka munyiwa Jihar mu da kasar mu addu’a Kan matsalar tsaro da ya addabemu a Jiha da Arewa baki daya.

Idan baku manta ba Gwamnati Jihar Nejan ta Zaftare wa ma’aikatan Jihar albashi kashi 30% cikin 100, Inda gwamnatin Jihar ta kafa hujja da cewa kudin da ake turowa Jihar daga gwamnatin Tarayya ya ragu dalilin Matsin Tattalin Arziki da ya shafi Kasar a halin Yanzu.

A ranar laraba ne Kungiyar Kwadago a Jihar ta sanar da ma’aikatan Jihar Tsunduma yajin aikin sai baba ta gani da lilin rage albashin ma’aikan ba bisa ka’ida ba Inji Ta.

Har yau Juma’a ma’aikatan Suna yaji Aiki a fadin Jihar, sai dai gwamnatin Jihar ta sanar da cewa Tana bukatar zaman Sulhu da kungiyar ta Kwadago a Jihar.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button