Labarai

Ma’aikatan babban bankin Najeriya CBN sama da mutun dubu da Dari biyar 1,500 ne za su koma aiki a ofishin bankin na Legas a ranar Juma’a Mai zuwa.

Spread the love

Wannan sabon ci gaba na zuwa ne biyo bayan matakin da sabon shugaban hukumar ya dauka na mayar da wasu sassan ma’aikatun CBN zuwa cibiyar tattalin arzikin kasar domin kare lafiyar ma’aikata, da kara yawan aiki da kuma rage cunkoso a babban ofishinsa.

CBN ya ce ya zama wajibi a dauki matakin da wasu abubuwa da suka hada da bukatar daidaita tsarin bankin da ayyukansa da manufofinsa da kuma raba fasahohin don tabbatar da yaduwar hazaka.

Ya kuma kara da cewa yana bin ka’idojin gine-gine, kamar yadda aka yi ta gargadin manajan ginin, da kuma bincike da shawarwarin kwamitin rage cunkoso na babban ofishin CBN.

Takardar da aka rabawa ma’aikatan ta ce, “Wannan shine don sanar da dukkan ma’aikatan babban ofishin babban bankin na CBN cewa mun bullo da wani shiri na rage cunkoso da aka tsara domin inganta yanayin gudanar da bankin.

“Wannan yunƙurin yana da nufin tabbatar da bin ka’idodin aminci na gini da haɓaka ingantaccen amfani da sararin ofis ɗinmu.”

Rahotanni sun bayyana cewa sassan da gwamnan babban bankin na CBN, Yemi Cardoso ya ba da takardan sauya sheka sun hada da sa ido kan harkokin banki, da sa ido kan cibiyoyin hada-hadar kudi, sashen kare hakkin masu amfani da kayayyaki, sashen kula da tsarin biyan kudi, da kuma sashen dokoki na kudi.

Duk da cewa kungiyar dattawan Arewa da wasu kungiyoyin Arewa sun yi Allah-wadai da matakin, wakilinmu ya tattaro cewa gwamnan CBN ya kuduri aniyar aiwatar da shi, domin ana sa ran za a rage ma’aikata 2,733 daga 4,233.

Wasu ma’aikatan da abin ya shafa sun fara komawa Legas.
“Wasu sun riga sun yi gaba. Sama da kashi 80 cikin 100 na ma’aikatan Sashen Sa ido na Banki an sake tura su aiki kuma iri daya ne ga Sashen Biyan Kuɗi,” inji majiyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button