Ilimi

Ma’aikatar Ilimi ta kasa ta fitar da ranakun da za’a fara jarrabawar NECO da NABTEB

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken jadawalin karatuttuka daban-daban na makarantun kasar nan ga Yan Ajin karshe masu fita daga sakandare daga ranar 17 ga Agusta zuwa 18 ga Nuwamba, 2020

‘karamin Ministan ilimi Hon. Chukwuemeka Nwajuiba ya bayyana haka a yau a Abuja bayan taro da sukayi da manyan shugabannin hukumomin jarrabawa a kasar Nan

yace Hukumar shiryawa jarrabawar yammancin afirika (WAEC) za ta fara ne a ranar 17 ga Agusta, 2020 yayin da
Jarrabawar (NABTEB) zai fara ne daga 21 ga Satumba kuma ya ƙare 15th Oktoba 2020
.
jadawalin ya nuna cewa Jarrabawar kammala sakandare ta Makarantun Sakandare na nijeriya (NECO) za’a fara ne daga 5 ga Oktoba kuma A ƙare ranar 18 ga Nuwamba, 2020.

Sanan jarrabawar Takardar Ilimin Firamare, (BECE) dana JSS 3 shi ma da Hukumar (NECO) take gudanarwa zai fara ne daga 24 ga watan Agusta kuma ya ƙare a ranar 7th ga Satumba, 2020

Bayan haka, Jarrabawar Kasa ta (NCEE) wacce jarabawa ce ta kwana daya wacce NECO take yi don nufin masu neman shiga Kwalejin Unity (JSS1) za su gudana a tsakanin ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2020.

Yin rijistar NECO (SSCE), wanda yake ci gaba, zai ƙare ranar 10 ga Satumbar, 2020 kuma ba za a ƙara tsawaita wajan yin rijistar ba

Bayanin ya ci gaba da nuna cewa Hukumar Kula da Larabci da Nazarin Addinin Musulunci (NBAIS) za ta fara jarrabawar ta a ranar Laraba, 23 ga Satumba zuwa zuwa 17 ga Oktoba, 2020

haka Ministan ya umarci dukkan bangarorin jarrabawar da su fitar da cikakkun bayanai game da jadawalin takardun karatun su a cikin kwanaki bakwai masu zuwa

An gabatar taron ne wanda Mai Girma Ministan Harkokin Ilimi ya jagoranta tare da Sakatare Janar na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Arc. Sonny Echono, magatakarda, Hukumar Kula da (JAMB), Farfesa Is-haq Oloyede; Magatakardar hukumar (NECO), Farfesa Godswill Obioma; Magatakarda, Hukumar Binciken Kasuwanci da Fasaha ta Kasa, (NABTEB) Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe; shugaban hukumar Larabci da Nazarin Addinin Musulunci, (NBAIS) Dr. Raji da sauran shugabanin hukomomin jarrabawa na nijeriya Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button