Ma’aikatar Tsaron Kasa Ta Ce Tana Yin Bincike Kan Jita-Jitar Kai Harin Boko Haram A Abuja.
Kakakin ma’aikatar tsaron kasa John Enenche yayi kira ga mazauna garin Abuja da su kwantar da hankalinsu, kuma ana gudanar da binciken jita-jitar da ke yawo kan cewa wasu ‘yan bindiga na Boko Haram za su kai hari a birnin.
Wata takardar sirri da aka samu ce daga ofishin hukumar Kwastan ta kasa, ke dauke da bayani da ke gargaɗin jama’a kan cewa, an samu rahoton Boko Haram na kakkafa wasu sansanoni a dazukan dake kewaye da Abuja, domin shirin afkawa babban birnin da kuma jihohin Nasarawa da Kogi.
Takardar ta kunshi sunayen wasu wurare da aka ce Boko Haram na kafa sansanoni a cikin yankunan Abuja da kuma wasu yankuna da ke cikin jihohin nasarawa da Kogi.
Jama’a da dama sun razana matuka bayan jin wannan bayani, inda suka yi ta zaman zullumi domin rashin tabbas kana bin da ka iya faruwa.
Ma’aikatar tsaron kasa ta ce jama’a su kwantar da hankulansu, kuma ana daukar dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro a cikin babban birnin da kewaye.
Daga Haidar H Hasheem Kano