Ma’anar kalmar almajiri Kashi na biyu

Spread the love

Kamar yadda na fada muku a baya zuwan Boko shine ya rikirkita harkar Makaratun Allo Arewa da ma sauran wasu Al’umara acikin Rayuwar Bahaushe, ada can kafin zuwan Boko Hukuma wato sarakuna sune ke kula da harkokin Makarantun Allo tana sa Ido kwarai da gaske domin ganin Basu shiga tagayyara ba sannan Bata gari Basu samu kofar shiga su lalata harkar ba, kafin zuwan Boko manyan Attajiran gari sune ke bawa Almajirai wuraren kwana a gidajensu ciki har da sorayen gidajensu ko nace Zauruka,Kafin zuwan Boko duk wani Magidanci zaka samu adadin wasu Almajirai suna zuwa gidansa karbar Abinchi har zakaji ana cewa Almjirin Gidan wane Kuma sannan shi kansa Magidanci zakaji Yana cewa Nima Dana Yana gari kaza Yana karatun Allo, Wato abubun suna da yawa matuka da gaske sai dai kawai Abunda zamu iya cewa a takaitattun Kalmomi shine akwai Amana da kulawar gaske tsakanin Almajirai da Mutanen gari kafin Zuwan Boko.

Zuwa Boko ya kwace ikon tafikar da Al’umma daga hanun sarakuna zuwa hanun wani tsari daban da ake Kira Gwamnati basai nayi Karin bayani ba me karatu yason me ake nufi da gwamnati sannan Kuma Boko bata bar Mutane haka ba sai da ta gadar musu da wani Abu da ake Kira ROWA, Boko Babu ruwanta da Kowa sai danta Ma’ana Wanda ke cikin tsarin Boko, Bazaka taba Zama cikin kunshin Hukuma ba sai kazama Dan Boko wannan rowa kenan, Rayuwa Kai kadai Babu ruwanka da Kowa bakason Kowa ya rabeka wannan ma Rowa ce Kuma Boko ta kawo hakan, Gina Gida Dan karami daga Kai sai Matarka Babu wadatattcen Zaure/Soro wannan ma Rowa ce ko Kuma kaga Gida tafkeke an Gina Amma idan kashiga kaga yan dakunan dake ciki sai abun ya baka mamaki wannan ma Rowa ce Kuma Boko ya kawo ta, Kididdige Abinchin da za’a dafa a Gida wannan ma Rowa ce wacce Boko ya kawo ta, bazan iya kawo muku dukkanin kalar Rowa da Boko ya kawo ba saboda suna da matukar yawan gaske kuma har Gobe suna cigaba da cutar da Al’ummar Arewa.

Wadannan abubuwa da suka faru sune suka jefa harkar karatun Allo cikin matsanancin Hali Wanda yasa ala tilas dalibanta wato Almajirai suka fara bara, hakan ya faru ne lokacin da wasu Malamai da Almajiransu Suka shigo Arewa daga kasar Algeria sukazo sukaga Komai ya lalalace shine Suka fara tura dalibansu bara domin su samo musu Abinchin da zasu ci, tunaninsu shine Komai lalacewa al’amura baza’a rasa na Allah ba cikin Al’umma wannan yasa ita kanta Barar zakaji ana cewa Allazee-Wahidin wato Allah daya yake jin hakan zakaji tausayi yazo maka sai ka bawa Almajiri sadaka. Abubuwan sun cigaba da tafiya a haka Babu sauki sai Kara Tabarbarewa hakan tasa wasu Matasan Malamai yan gari Suka fara bude Makaratun Islamiyya suna jinginawa da Boko ko Kuma nace sukayi tsarin Boko suka ware azuzuwa da fannoni daban-daban wala’Allah mahukuntan Yan Boko zasu kawo musu Dauki sai dai babbar matsalar da suka samu itace Suma Mafi yawan Azuzuwansu sorayen Mutanene dole tasa Suma suka Fara Bara ammafa ba ta Abinchi ba su Barar kudi sukeyi, yadda abun yake shine Sukan ware wani lokaci suce zasu gudanar da saukar karatun Alkura’ani su gayyato manyan Mutane masu Kumbar Susa a Gwamnati domin suyi Barar Filin da zasu Gina makaranta ko Kuma Barar kudaden da zasu sayi kayan aiki, wani lokacin akan dace wasu masu tsoron Allan suna bayarwa wasu kuwa suyi Alkawari su kasa cikawa wasu kuwa sai su turo wakili zuwa wannan wuri domin kada ace sunyi Abun kunya an tambayeshi Abu sun kasa Badawa alhali suna dashi wasu kuwa Sukan kekashe zuciyarsu zuzo wurin amma bazasu bada Komai ba wasu Kam ma ko wurin basa zuwa.

Yau anan tsan tsaya sai wani lokacin zanci gaba Insha’Allahu Amma kafin nan ga jerin wasu Tambayoyi da zanyi Kuma Ina son Kowa ya amsamin daidai fahimtarsa domin suna da Alaka da Rubutu na gaba.

1, shin me kake Tunani idan Gwamnati ta janye dukka Tallafin da take bawa Makaratun Boko ta barsu daga iyaye sai Malamai sai Kuma Dalibansu musamman Makarantun Kwana??

2, Ance Bara haramunce a Addinin Islama Shiyasa za’a Hana Karatun Allo to menene Hallacin Makaratun Boko na Kwana na Yaya mata?

3, A Tunaninka irin Ta’asar da akeyi a Makaratun kwana na Yan Mata Bata zarce Barar da Almajirai keyi ba illah?

4, Da ka tura Danka Makarantar Allo yaje yayi Barar Abinchin da zaici da Kuma ka tura yarka Makarantar kwana taje ta Zama Yar Madigo wanne ne yafi illa a Addinin Musuluncin?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *