Labarai

Mafiya yawan motocin da jami’an tsaro suka kwashe daga gidajena guda biyu da ke Gusau da Maradun, na sayo su ne kafin na zama gwamna – Bello Matawalle

Spread the love

Matawalle dai na mayar da martani ne a kan farmakin da jami’an tsaro da suka kunshi ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka kai gidan sa ranar Juma’a.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce yawancin motocin da jami’an tsaro suka kwashe daga gidajen sa guda biyu da ke Gusau da Maradun, an sayo su ne kafin ya zama gwamna.

Matawalle dai na mayar da martani ne a kan farmakin da jami’an tsaro da suka kunshi ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka kai gidan sa ranar Juma’a.

Mun rawaito yadda jami’an suka je gidan tsohon gwamnan suka fara kwashe motocin.

Sai dai da yake zantawa da BBC Hausa a ranar Asabar, Matawalle ya zargi jami’an tsaro da wawashe kayan matansa da ‘ya’yansa, ciki har da kayan sawa.

Ya ce ba a ba shi kwafin umarnin kotu ba wanda ya baiwa jami’an tsaro damar mamaye gidansa kamar yadda magajinsa Dauda Lawal ya yi ikirari.

“Na dade ina sana’ar mota kuma akasarin motocin jami’an tsaro suka kama daga gidajena biyu, wadanda na siyo daga Amurka tun kafin na zama gwamna ne,” in ji tsohon gwamnan.

Ya ce wasu daga cikin motocin da aka tsare a gidansa da ke Maradun, masu hannu da shuni ne suka bayar da su, kuma dukkansu suna dauke da hotunan shugaba Tinubu da kansa.

“Motocin da suka kama a Maradun, wadanda masu hannu da shuni ne suka ba ni gudummuwa, kuma duk suna dauke da hotona da na Bola Ahmed Tinubu. Amma abin mamaki sai suka ce motocin na gwamnatin jihar ne,” inji shi.

Da yake mayar da martani ga ikirari da jami’an tsaron suka yi na cewa an kwato motoci 40 a gidansa, Matawalle ya ce, “Jami’an tsaro su baje motocin guda 40 domin yanke hukunci ga jama’a ba. Duk wanda ya san Bello Matawalle zai yarda cewa ni ina sana’ar mota tun lokacin da na zama Gwamnan Jihar Zamfara.”

Ya kuma yi zargin cewa jami’an tsaron sun wuce kwato motoci inda suka dauko kayayyaki masu tsada da na matansa da na iyalansa.

Tsohon gwamnan ya ce yana Abuja kuma babu wanda ya kira shi ya sanar da shi cewa ana bukatar kulawar sa dangane da lamarin. “Amma abin da na ji shi ne jami’an tsaro sun mamaye gidajena a kashin kansu kamar babu doka da oda a Najeriya,” in ji shi.

Matawalle ya ce ba zai nemi jami’an tsaro ko gwamnatin jihar su dawo da motocin ba, a karshe ya ce, “Duk da haka zan bi hanyar da ta dace kamar yadda doka ta tanada.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button