Labarai

Maganar Na Kusa da Shugaba Buhari ya kamu da Corona, Karya ce kawai~ Mal. Garba Shehu.

Spread the love

Fadar Shugaban kasa tana so ta ba ’yan Najeriya shawara ta bakin Garba Shehu, da su yi biris da labaran kanzon kurege wadanda wasu ke kokarin yada labaran karya ga jama’a.

Munyi martani game da mummunan karya da wulakanci, wani rahoto da ake kira jaridar Digital wanda, a jiya Laraba, ta yi ikirarin cewa mai taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari, Sarki Abba yana da COVID-19.

Wannan rahoton karya ce kawai kuma kokarin tada zaune tsaye ne ta yada labarai ta yanar gizo don yaudarar jama’a.

Bayan umarnin likitoci da masana kimiyya da kuma kula irin na Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban Ma’aikatan, duk ma’aikatan da ke aiki ga Shugaban Kasa da kewayensa, ana bincikar lafiyarsu a kai a kai domin duba kwayar cutar. Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Jama’a da Al’amuran Cikin Gida, Sarki Abba, wanda makaryata ke yayata yana dauke da Corona Virus, yana yawan fama da Rashin Lafiya amma ba Corona Bace.

Shehu yace yana shawartar jama’a da suyi watsi da irin wadannan labaran da akeyi da nufin batar da mutane da kuma haifar da damuwa tsakanin al’ummar kasa da nufin Jingina Rashin lafiya ga Shugaba Buhari.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button