Sana'o'i

Magidanci mai Sana’ar Yankan Farce

Magidanci Ya Rike Ya’ya Takwas Da Mace Daya Da Sana’ar Yankan Farce.

Sana’a Sa’a, Jaridar Mikiya ta Zanta Da Wani Magidanci Mai Sana’ar Yankan Farce.
Malam Ya’u Amadu Magidanci ne daya Shekara goma sha Uku Yana Sana’ar Yankan Farce, da wannan Sana’ar tasa har yayi iyali yake Kuma cigaba da Rayuwar sa.
Mikiya: dafarko zamu So ka bayyanawa Masu Sauraron mu, Sunan ka da tarihin ka a taqaice?
Malam Ya’u: Sunana Ya’u Amadu an Haife ni a karamar hukumar Suleja, Jihar Niger, na taso nayi yawan Karatun Alqur’ani a Garuruwa daban daban, yau ina da shekara hamsin da hudu a Duniya.
Mikiya: Cikin bayanin ka kace kayi Yawon Karatun Qur’ani Mai girma, Kenan Malam Ya’u beyi Karatun Boko ba?
Ya’u: Baza a ce ba a yi ba, an Dan taba, na yi primary, a inda aka haife ni, nafara Sikandire a zariya Ina aji hudu, muka tafi gabas Neman Alqur’ani mai girma.
Mikiya: malam Ya’u gashi yanzu kana da Shekaru har wajen 54, shin da wacce Sana’a ka Dogara, har kake ciyar da iyali, Kuma kake Rayuwar Yau da kullum?
Ya’u: (dariya) nayi sana’o’i dayawa a Lokacin kuruciya, amma yanzu Sana’ar da nakeyi, Kuma na Dogara da’ita, itace Sana’ar Yankan farce, yau shekarata goma sha Uku Ina yin ta.
Mikiya: malam Ya’u Menene sirrin wannan Sana’a har aka shekara 13 ana yinta?
Ya’u: (dariya) kowacce Sana’a sirrin ta daya ne, shine rufawa Kai asiri, ace yau ba a Ga malam Ya’u a kofar gidan wani alaji ba, Yana Neman kudin ragon suna, ko Neman kudin Magani iyali Bata da lafiya ba.
Mikiya: yazuwa yanzu na san anada Mata da Yara ko sun Kai nawa?
Ya’u: Ta farko ta rasu, yanzu muna zaune da Mata daya ne, Yara takwas
Mikiya: Allahu Akbar Allah yaji qanta, a Yanzu malam Ya’u Yana iya daukar Nauyin Mata da Ya’yansa takwas da wannan Sana’ar, shin malam Ya’u ba ya Hadawa da wata Sana’ar?
Ya’u: Bana wata Sana’a sai dai Noma a shekara-shekara.
Mikiya: ko malam Ya’u zai Iya bayyanawa Masu Karatu nawa yake samu a rana daya a wannan Sana’ar ta yankan farce?
Ya’u:(dariya) babu lissafi, amma dai za kaci kasha, Kuma kayi Zumunci, Albarkacin Sana’ar alhamdulillah babu abin da zamu ce Sai godiya.
Mikiya: malam Ya’u Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button