Magoya bayan Atiku sun ce ya zama dole a Kori Wike daga jam’iyar PDP domin shine matsalar jam’iyar a yanzu.
Daraktan Bincike da Dabaru na Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a 2023, Atiku Abubakar, Dokta Don Pedro Obaseki, ya ce korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike daga PDP aiki ne da ya zama dole a yi shi. tsira jam’iyyar.
Ya bayyana cewa kiran da Wike ya yi na a dakatar ko a kore tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, cin zarafi da ya yi wa a jam’iyyar da kuma cin amana da ya yi ya kamata a kore shi.
Obaseki ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a Abuja, ranar Litinin.
A cewarsa, Wike wanda har zuwa lokacin da aka nada shi minista a matsayin gwamnan jihar Ribas, yana da hannu a cikin mafi yawan rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP saboda tsananin kishinsa na ga rashin Nasara a jam’iyyar.
Ya yi nuni da cewa Wike bai ji dadi ba tun bayan makircin da ya fara da goyon bayansa ga Uche Secondus na shugabancin jam’iyyar da abubuwan da suka kai ga kayar da shi a zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP.
Obaseki ya ce, “Wike shine matsalar PDP kuma korar Wike yanzu aiki ne da PDP zata yi.”
Da yake mayar da martani ga kiran da Wike ya yi na a fitar da Atiku daga PDP, Obaseki ya ce, “Wanda ya cancanci a kore shi daga jam’iyyar shi ne mutumin da ke kira da a kori wasu daga jam’iyyar.
“Wike shine wanda ya kirkiro wata kungiyar asiri a cikin jam’iyyar kuma ya kira ta da G-5. Sabi da son rai wanda Kuma ya yi kamfen na adawa da jam’iyyar.