Magoya bayana Ku kwantar da hankalinku zamu tabbatar Hukumar zabe tayi mana Adalci ~Cewar Gawuna.
Dan takarar gwamnan jihar Kano ta Bakin kwamishinan yada labarai Garba Mohammed a wata sanarwa Yana Mai cewa Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankulansu su kasance masu bin doka da oda ko da kuwa sakamakon sake duba sakamakon zaben gwamna da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.
Ya ce jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa a cikin tanadin doka da sauran hanyoyin da aka shimfida domin ganin an yi adalci a lamarin.
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa da dan takarar gwamna Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa sun bayyana gamsuwarsu da yadda ‘yan jam’iyyar ke gudanar da rayuwarsu kafin zabe da lokacin da kuma bayan zabe.