Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno yayi fallasa, ya ce kudaden da aka bawa tsofaffin hafsoshin tsaro sun bace.
Mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno yace akwai wasu kudade da aka baiwa tsofaffin hafsoshin tsaro sunyi batan dabo.
A cewar Monguno, yace an bada wadannan kudaden ne don sayen kayan yaki, don karfafa yakin boko haram, Monguno yayi wannan fallasa ne a hirar da akayi da shi yau Juma’a 12 ga watan Maris a ofishin Sa dake Babban birnin tarayya Abuja.
Monguno yakara da cewa sababbin hafsoshin tsaron da Buhari ya Nada kwanakin baya sunce basu ga kudaden ba, kuma basuga makaman da aka CE a saya dasu ba.
Munguno ya CE babu shakka babu Wanda yasan abinda akayi wadannan kudaden, amma da yardar Allah zasu binciki yadda akayi da wannan kudaden.
Munguno yace tunda ba afara binciken ba don haka babu wani abu dazai fara cewa, amma tabbas kudi dai sun salwanta, kayan da aka CE a saya dasu ma ba a gansu ba, sababbin hafsoshin tsaro sun CE suma fa basuga wasu kayayyakin tsaro da ake magana akai ba.
Allah ya sawwake.
Daga Kabiru Ado Muhd