MAI HANKALI SHIKE GANE FURFURAR FARAR TUNKIYA

Idan ka ɗauki gwamnatin Shugaba Buhari rankacakaf! ka ɗorata a bisa mizanin gaskiya da adalci babu wani abu ɗaya tilo wanda mutum zai bugi ƙirji ya nuna a matsayin abin da talaka ɗan talaka mai siyar da yalo da goba yake amfana kai-tsaye face shirin N-POWER.
-A ƙarƙashin shirin matasa da yawa sun bar zaman kashe wando sannan sun samu aikin dogaro dakai
-A ƙarƙashin shirin ilmi ya farfaɗo sakamakon yadda makarantu suka samu wadatattun malamai masu jini a jika.
-A ƙarƙashin shirin matasa da yawa suke kulawa da iyalansu, iyayensu tare da taimakawa ƴan uwansu.
-Ƴan N-Power da yawa sunyi rawar gani ta fuskar kawo cigaba da magance matsalolin garuruwansu
-Ƴan N-Power da yawa basu da wani abu da suke ciyar da iyalansu sai ta alawus ɗin da suke samu duk wata.
-Ƴan N-Power da yawa sun samu horo da gogewa ta fuskar koyarwa , shi yasa ɗalibai suke samun ilmi ingantacce a makarartunmu
-Korar ƴan N-power babbar barazana ce ta fuskar zaman lafiya da tattalin arziƙin ƙasa
-Korar ƴan N-Power zai iya kawo cikas ga fannin ilmi a ƙasa
Duba da irin waɗannan abubuwan dana zayyana a sama, Duk da bana cikin shirin N-Power ina ganin ba karamin kuskure bane a kori bayin Allah nan a rana tsaka. Gwamnatin Najeriya ta yiwa matasan nan adalci a matsayinsu na ƴan ƙasa ta barsu su cigaba da aikinsu ko kuma gwamnatocin jahohi su duba Allah su basu aikin yi na din-din-din.
Tabbas ƙara ɗaukar sababbin ƴan N-power abu ne daya dace amma korar waɗanda suke cikin shirin ba ƙaramin kuskure bane da cefa al’umma cikin ƙuncin rayuwa musamman ma matasa manyan gobe.
Daga Mutawakkil Gambo Doko