Kungiyoyi

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Ya Zama Uban Kungiyar “Arewa Media Writers” Na Kasa Baki Daya (Grand Patron).

Spread the love

A yau Laraba Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban Kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, ta kai ziyara fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, tare da kaddamar da shi a matsayin uban kungiyar na kasa baki daya (Grand Patron), bayan kammala taron da kungiyar ta yi a jihar Kano, yayin ziyarar wasu daga cikin shugabannin kungiyar na kasa sun halarci taron da shugaban kungiyar reshen Jihar Kano Umar Kabir Dakata, tare da sauran shugabannin kungiyar reshen jihar da Membobin Kungiyar na sassan jihohin yankin Arewa masu yawa.

Bayan kammala taron Kungiyar ta nada mai martaba Sarkin ne a matsayin uban kungiya na kasa, duba da irin gudunmawar da yake baiwa al’ummar yankin Arewa baki daya a matsayin sa na mai rike da sarautar gargajiya mai daraja, a wannan yanki namu na Arewa.

A yayin ziyarar Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi maraba da wannan Kungiya bisa ziyarar da ta kawo masa kafa da kafa, sannan ya jinjinawa wadanda suka kafa kungiyar tare da yaba musu kan irin namijin kokarin da sukai.

Mai martaba Sarkin Kano ya bayyana cewa, Social Media guri ne mai muhimmanci, a wannan zamani namu, Sarki yace mafi yawancin jama’a, hankalin su ya koma kan kafafen yada labarai, saboda haka Sarki yai kira ga wannan kungiya da ta cigaba da abubuwan da ta sa a gaba, domin abubuwa ne masu kyau.

Sarkin ya ce, yana tare da wannan Kungiya sannan ya yi alkawarin bata gudunmawa ta kowane fanni, domin cigaban yankinmu na Arewa, a karshe mai martaba Sarki, ya yiwa kungiya fatan Alkhairi tare da fatan Allah ya kara daukaka ta.

A jawabin shugaban Kungiyar na kasa, Comrade Abba Sani Pantami, ya mika godiya zuwa ga mai martaba Sarkin, bisa Amincewa da wannan kungiya da yayi, kuma ya karbeta hannu biyu biyu, sannan ya godewa mai martaba Sarkin sakamakon yadda yake taimakon Arewa da yan Arewa baki daya.

A karshe shugaban Kungiyar, ya yiwa Sarkin na Kano alkawarin cigaba da jajircewa dan ganin an samarwa da yankin Arewa cigaba ta kowane fanni.

Haka zalika Kungiyar ta yi kira ga Al’umma da su bawa kungiyar hadin kai tare da goyon baya, domin kawo wa yankin Arewa da Najeriya baki daya cigaba.

Kungiyar “Arewa Media Writers” tana bukatar Addu’o’i daga gareku Allah ya shige mata gaba kan muhimman ayyukan da ta saka a gaba. Amin.

Daga Kungiyar “Arewa Media Writers”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button