Maida Yan Gudun Hijira Garuruwansu Tamkar Jefa Tumaki Ne Ga Damisa, Gargadin Sanata Shehe Sani Ga Gwamna Zulum.
Sanata Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dokoki ta kasa ya gargadi gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum game da mayar da ‘Yan Gudun Hijira (IDPs) zuwa mahaifarsu.
Tsohon dan majalisar a cikin wani sako da ya gabatar a safiyar yau Asabar a shafinsa na Twitter, ya bayyana gwamnan jihar ta Borno a matsayin mutum mai jarumtaka, maras haushi kuma mai son jama’a amma bai yarda da shirinsa na sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar su koma yankinsu ba.
Ya koka cewa shirin Zulum na tsugunar da ‘yan gudun hijirar za a iya kamanta shi da’ jefa tumaki ga Damisa ‘. Ya rubuta:
“Gwamnan Borno mutum ne mai kazar-kazar, mai kaunar mutane. amma maida ‘yan gudun hijira garuruwansu jefa Raguna ga Damisa.” (@ShehuSani) Oktoba 3, 2020.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a makon da ya gabata ya maida sama da mutane dubu daya da suka rasa muhallinsu a garin Baga da ke arewacin jihar ta Borno.
Bayanin da aka tattara ya nuna cewa sama da mutane dubu daya da suka rasa muhallansu sun dawo gida a ranar Asabar.
An baiwa wadanda suka dawo din kyautar naira dubu goma (N10,000) da buhun shinkafa kowannensu don fara rayuwa cikin sauki.
Rahoton ya bayyana cewa Gwamna Zulum ya kasance a garin Baga ranar Juma’a, ya kwashe dare biyu tare da wadanda suka dawo din karkashin kulawar tsaro sosai don sa ido kan shirye-shiryen sake tsugunar da su a garin na kasuwanci, wanda tun farko ‘yan bindiga suka mamaye.
Gwamnan na Borno a cikin bayanin nasa ya yi kira ga wadanda suka dawo din su kasance masu bin doka da oda kuma su ba da goyon baya tare da hada kai da jami’an tsaro a wasu don jin dadin kariya da amincin su.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta yi watsi da su ba amma za ta ci gaba da tabbatar da cewa sun ba su kariya sosai.
Sojojin na Najeriya sun kuma nuna cikakken goyon baya ga kokarin da Gwamnan Jihar Borno ke yi na dawo da ’yan gudun hijirar jihar zuwa garuruwansu.
Wannan bayanin ya fito ne daga ofishin Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Hedikwatar Sojojin Nijeriya da ke Abuja, Kanar Sagir Musa, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Maiduguri a ranar Talata, ya bayyana matakin da Gwamna Zulum ya dauka a matsayin “matakan da suka dace a inda ake so. ”.
Kanal Musa ya kara da cewa, “Sojojin Nijeriya suna ba da cikakken goyon baya ga kokarin da Gwamnan Jihar Barno, Farfesa Babagana Umara Zulum ke yi, na sake tsugunar da’ yan uwanmu ’yan kasa da matan da suka rasa muhallinsu a cikin jihar zuwa gidajen kakaninsu.
“Gaskiya kokarin gwamnan abin a yaba ne kuma matakan da suka dace a inda ake so.”