Labarai

Mailafiya Ya Amsa Gayyatar DDS Kan Maganar Da Yayi Cewa Wani Gwamnan Arewa Ne Kwamandan Boko Haram.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Obadia Mailafiya da yayi ikirarin cewa akwai gwamnan Arewa dake kwamandan Boko Haram kuma hukumar ‘yan sandan farin kaya ta DSS ta gayyaceshi. A yau ya amsa gayyatar, kamar yanda hutudole ya samo.

Mailafiya ya amsa gayyatar inda yaje ofishin DDS na Jos tare da lauyansa, Pius Akumbo(SAN) sai kuma shugaban kungiyar lauyoyin jihar Filato.

A lokacin da suka isa bakin ofishin DSS din kungiyoyi da dama masu goyon bayan mai lafiya da mutane magoya bayansa da dama musamman daga tsakiyar Najeriya sun yi dandazo a kofar ofishin.

Duk da jami’an DSS dake mazurai, Tribune ta ruwaito cewa magoya bayan Mailafiya sun ki ko gezau inda suka ce ba zasu bar wajan ba sai Mailafiya ya fito daga cikin ofishin DSS din.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button