Labarai

Majalisar Dattawa ta ce Zata kara Kawo kudurin Buhari ya Sallami Hafsoshin Tsaron Kasar Nan.

Spread the love

A dai dai lokacin da Matsalar Tsaro ke kara ta’azzara yan Majalisun Dattawa sunce zasu kara Kai kudurin su gaban Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin ya sallami Shuwagabannin Tsaron kasar Tunda sun Gaza.

A watan da ya gabata ma majalisar ta yi kira ga Shuwagabannin Tsaro da suyi Murabus ko Buhari ya sallamesu tunda Sun Gaza kawo Karshen Matsalar Tsaro a Yan kin Arewa.

Sai dai Shugaba Buhari ta bakin Mai taimaka masa Malam. Garba Shehu ya matarwa majalisar martani da kakkausar murya, Inda yace Babu wanda Ya Isa ya cire Hafsoshin sai Shugaba Buhari ya ga dama.

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, mah yayi Kiran Shugaba Buhari da ya Kwashe Sojiji a Yankin Jihar Zai yi amfani da ‘Yan Sanda da ‘Yan Sakai domin kawo karshen Boko Haram a Yankin.

Zulum din ya Zargi Sojojin Kasar da Cin amanar Sa wajen yaki da Boko Haram, Sai dai Shugaba Buhari Yayi Biris da Kudurin na Zulum.

Har Ila yau Gwamnonin Arewa sun Garzaya Fadar shugaba Buhari da Irin wannan Bukatar Sai dai Shugaba Buhari ya Biris da Bukatarsu.

Sai dai a Nasu bangaren Sojojin Kasar Suna Ikirarin Suna samun Nasara Sosai kan ‘Yan Ta’adda a Yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, Sai dai Al’ummar Kasa Na Ganin Wannan Ikirarin Na Soja Ba Gaskiya bane.

Masa Sunce Tunda ake Shuwagabanni kasa a Kasar Nan babu wanda ya Baiwa Shuwagabannin Tsaro Makudan Kudi domin Shawo kan Matsalar Tsaro, Amma Kwalliya bata biya Kudin Sabulu Ba.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button