Ilimi

Majalisar Dattawa Ta Kalubalanci Matakin Gwamnatin Tarayya na Dakatar da Rubuta Jarrabawar WAEC.

`Yan Majalisar dattawa sun kalubalanci hukuncin gwamnatin tarayya na kin bude ajujuwan karshe na Makarantu don rubuta jarrabawar WAEC.

Kwamitin mai kula da makarantu na matakin farko ya kalubalanci hukuncin da katar da Dalibai daga rubuta jarrabawar WASSCE wacce WAEC ke shirya wa ta shekarar 2019/2020.

Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar Covid-19 a farko-farkon watan yuni ne ya sanar da cewa zai bude ajujuwan karshe na Makarantu don rubuta jarrabawa. Wanda ya hada da ‘yan aji 6 na Pramare, yan sakandre matakin farko aji 3 da ‘yan sakandre matakin karshe aji 3

Daga bisani, karamin ministan ilimi Nwajiuba, a yayin zanta warsa da manema labarai, ya sanar da cewa, jarrabawar WASSCE 2020 za ayi ta ne tsakanin 4 Ga Augusta zuwa 5 Ga Satumba.

Amma, sai gashi Ministan Ilimi Adamu Adamu ya sanar da cewa, duk makarantu zasu cigaba da zama a kulle har sai lokacin da akaga yafi dacewa a bude makarantun. Kuma ministan ya nemi gwamnonin jihohin dasuka fara shirin bude makarantun dasu dakata.

A yayin mai da martani a wani shiri da aka gabatar mai taken “Bai dace a rushe WASSCE ba, shugaban kwamitin, Parfesa. Julius Ihonvbere, ya nuna rashin jin dadin sa game da hukuncin ci gaba da kulle makarantu.

Ihonvbere yace Kwamitin majalisa mai kula da karatu matakin farko, sun samu rahoto mai ban al’ajabi cewa, ministan ilimi yace Daliban Makarantar Nijeriya baza su rubuta jarabawar WASSCE ba ta shekaran nan.

Kuma bai gayawa mutanen kasa ba, ko wannan hukuncin da yayanke ya shawarci Shuwagabannin Kasashen Afirka Ta yamma ko kuwa ya nemi shawarar mahukunta jarrabawar ta WAEC ko Gwamnonin Jahohi da masu Ruwa da tsaki a fannin ilimi.

Wannan canza shawarar ba alheri bane a kasa. Don zai kawo rudani a cikin sha’anin ilimi a Kasar Nan.

Ko a dai dai lokacin da Ministan Ilmi ya Sanarda dakatar da Rubuta Jarrabawar WAEC Din Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Alh. Atiku Abubakar Ya kalubalanci Matakin Na Dakatar da Rubuta Jarrabawar ta WAEC.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button