Majalisar dattijan Nageriya batayi Tir da kalaman Gwamna El Rufa’i ba ~Sanata Uba Sani…
Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya Yace Majalisar Dattijai Bata yi tir da kalaman Gwamna Malam Nasir El-Rufai game da sake fasalin Nageriya ba kalaman Wanda Gwamnan yayi a bikin cika shekaru 50 da kafa gidan Arewa a Kaduna.
Kalaman da ake dangantawa ga Sanata Ajibola Bashiru ba suna nuna cewa matsayin majalisar dattawan ba ne. A.a Maganar Gaskiya ita Majalisar dattijai a kowanne lokaci ba ta umarci kowa da ya shiga wannan Batu dake tsakanin ta da Gwamna El-Rufai a kan kalaman nasa dangane da rahoton Kwamitin APC kan sake fasali, wanda ya jagoranta ba.
Sanata Uba Sani Yace Ni mamba ne na Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kafafen Yada Labarai kuma ina iya bayyanawa karara tare da tabbatarwa cewa ba a bawa ko wanne mamba na wannan kwamitin doka a hanunsa domin Wannan kalami ba.
Na kalli kyakkyawan bayanin da Gwamna El-Rufa’i ya gabatar kuma koke ne yayi ga Majalisar ta Tarayya kancewa da su hanzarta aiwatar da gyare-gyaren tsarin mulki amma Babu amfani a gina irin wannan koken amatsayin kamar hari ga Majalisar ta Dokokin Kasa. Don Haka Ra’ayoyin da Sanata Bashiru ya bayyana yayi Haka ne bisa ra’ayin kansa da kansa amma ba da yawun Majalisar ba… Inji Sanata Uba Sani