Labarai

Majalisar Dinkin Duniya da Turai sun gargadi jami’an tsaron Najeriya kan masu zanga-zanga

Spread the love

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Turai sun bukaci jami’an tsaron Najeriya da su kawo karshen musgunawa maso zanga-zangar EndSars.Kakakin sakatare janar na Majalisar, Stephane Dujarric ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, yayin da shugaban tsara manufofin kasashen ketare na EU Josep Borrell ya bukaci gudanar da binciken don hukunta jami’an tsaron da suka bude wuta kan masu zanga-zangar.

Kiran na zuwa ne bayan da jami’an tsaro da ba’a kai ga tantance su ba suka budewa masu zanga-zangar EndSars wuta, jim kadan bayan cikar wa’adin dokar hana fita a birnin legas.

Lamarin da ya ci cigaba da haifar da matsaloli a Lagos da wasu sassan kasar, ganin yadda yanzu haka aka ci gaba da kona gine-ginen gwamnati da na al’umma.

Tun a daren Talata kafin wayewar Laraba, fusatattun masu zanga-zangar EndSars da ta rikede, sun kona wani Babban Otel da wani asibiti baya ga ofisoshin ‘yan sanda.

Yayin da a wayewar garin yau Laraba aka cinna wuta a cibiyar Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA, da kuma gidan talabijin na TVC da ke Legas din, tare da ofishin Hukumar kiyaye haddura da wani sashe na sakatariyar Legas.

Kazalika, fusatattun masu zanga-zangar sun bankawa tashar motocin BRT na gwamnatin Lagas dake Oyingbo wuta, inda motocin Bus na safa-safa da dama suka kone, yayin da ake ci gaba da kai hari kan bankuna a wasu sassan birnin.

A bangare daya, bayanai sunce ankuma kona gidan mahaifiyar gwamnan jihar Baba Jide Sanwo – Olu, yayin da suka farma gidan sarkin Lagas, wanda yasha da kyar, kuma ‘yanzu haka ana cigiyar sanda girma na sarautar, bayan da yunkurin kona gidan ya ci tura da taimakon sojoji. Comr Zakari Ya’u Salisu, Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button