Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Sojoji Su Saki Shugaban Kasar Mali Cikin Gaggawa.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nemi da a saki shugaban kasar Mali da mambobin gwamnatinsa cikin hanzari ba tare da sharadi ba, a ranar Talata bayan da sojojin ‘yan tawaye suka kame su.
A cikin wata sanarwa da kakakin Guterres ya fitar ya ce “Sakatare-janar ya yi kakkausar suka kan wadannan ayyukan, ya kuma yi kira da a hanzarta maido da tsarin mulki da bin doka da oda a Mali,” in ji kakakin Guterres.
Kakakin rundunar, Stephane Dujarric ya kara da cewa, “Don haka, ya bukaci sakin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da membobin majalisar sa cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba saboda gudun sake barkewar rikice-rikice tsawon watanni a kasar Afirka ta yamma.
Guterres yana bin abubuwan da ke faruwa a Bamako babban birnin kasar “cikin matukar damuwa,” in ji Dujarric.
Babban magatakardar ya sake nanata kiran nasa na neman sasanta rikicin cikin lumana.
Kakakin ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki, musamman na tsaro da su yi taka tsantsan tare da kare hakkin dan adam da yancin kowa na dukkan ‘yan Mali, in ji kakakin.
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa kan rikicin a ranar Laraba da yamma, jami’an, diflomasiyya a New York sun ce Faransa da Nijar sun nemi wannan ganawar ne kuma za ta gudana ne a sirrince in ji wani jami’in diflomasiyya na Majalisar Dinkin Duniya da ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Faransa na AFP.