Labarai

Majalisar Nageriya ta barke da rikinci Kan gayyatar Buhari ya gurfana a gabansu.

Spread the love

A yau zaman da aka yi a zauren majalisar wakilai ya zama mai rikitarwa a ranar Talata yayin da mambobin majalisar suka samu sabani sosai kan kudirin da ke neman gayyatar Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bayyana a gaban ‘yan majalisar don yi musu bayani kan karuwar matsalar rashin tsaro a kasar.

Majalisar na nazarin wani kudiri da mambobinta daga jihar Borno suka gabatar game da kisan gillar da wasu ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi wa manoman shinkafa 43 a jihar.

Wani bangare kudrin shi ne gayyatar Buhari ya bayyana a farfajiyar majalisar ya yi wa ‘yan majalisar jawabi a zauren Majalisar

Kokarin shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila; Shugaban masu rinjaye, Alhassan Ado-Doguwa; da Shugaban Kwamitin Majalisar kan Sojan Sama, Shehu Koko, da sauransu, sun so a bar maganar

Rokon Gbajabiamila cewa ayi amfani da dokar ta baci maimakon haka shima an ki amincewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button