Labarai

Majalisar wakilai ta umarci ma’aikatu da su dawo da kudaden COVID-19 Naira Bilyan N85bn da aka ware a karkashin gwamnatin Buhari.

Spread the love

A yau ranar Alhamis ne kwamitin majalisar wakilai ta kasa, ya umarci ma’aikatar lafiya ta tarayya da ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari da su dawo da jimillar Naira biliyan 85 da aka ware musu a matsayin kudaden shiga tsakani na COVID-19.

Kudurin ya biyo bayan kudirin da Bassey Akiba dan jam’iyyar Labour ne daga jihar Cross River ya gabatar dangane da rashin halartar jami’an ma’aikatar a zaman binciken da aka yi ranar Alhamis.

A wata sanarwa ta baya-bayan nan, PAC ta kira Ma’aikatu da Hukumomi 59 da su bayyana a gabanta domin fara gudanar da bincike kan zargin cin zarafi da kudaden da aka yi niyyar yakar cutar ta duniya da aka fi sani da Coronavirus.

Tun a ranar Laraba 17 ga watan Janairu ne aka shirya ganawar tsakanin ‘yan majalisar da ma’aikatun, amma majalisar ta koma da zaman Zuwa ranar Alhamis domin jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Oyo sakamakon fashewar wani abu da ya faru ranar Talata a babban birnin jihar, Ibadan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button