Majalissar dokokin jihar Sokoto ta rage kudin aure, Majalissar ta ce kudin da ake kashe a aure almubazzaranci ne.

Mista Shehu, wanda shi ne Shugaban kwamitin, ya gabatar da rahoton kwamitin a zauren Majalissar, wanda aka amince da shi gaba daya ya zama doka.
A ranar Talata ne Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da kudirin dokar daidaita kudaden aure a jihar.
Kudurin dokar wanda Alhaji Abubakar Shehu (APC-Yabo) da Faruk Balle (PDP- Gudu) suka dauki nauyinsa, an mika shi ga kwamitin kula da harkokin addini na majalisar.
Mista Shehu, wanda shi ne Shugaban kwamitin, ya gabatar da rahoton kwamitin a zauren taron, wanda aka amince da shi gaba daya ya zama doka.
Kudirin dokar dai ya tanadi kula da yadda ake kashe makudan kudade wajen auratayya, suna, kaciya da sauran bukukuwan a fadin jihar.
Mista Shehu ya ce a lokacin da yake gabatar da rahoton, kwamitin ya gana da masu ruwa da tsaki da suka ba da gudummawa mai kyau a cikin kudirin.
Bayan tattaunawa a zaman da mataimakin shugaban majalisar Alhaji Abubakar Magaji ya jagoranta, ‘yan majalisar sun amince da kudurin gaba daya.
(NAN)