Addini

Majiyar tace Malaman Kano na kokarin zillewa Zaman mukabala da Sheikh Abdujabbar.

Spread the love

Rahotanni daga jihar Kano sun nuna Cewa Majalisar malaman jihar Kano na kokarin janyewa da Batun mukabala tsakanin Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara da Majalisar wata majiya da muka tuntuba dake kusa da Malam Abdujabbar ta Tabbatarwa da Jaridar Mikiya Cewa kawo yanzu Shirin Gwamnatin jihar Kano na shirya Zaman tattaunawar ya samu cikas Sakamakon turjiya da kin aminta da saka hannu a takardar gayyatar mukabala da Gwamnatin Jihar kano ta aikawa ko wanne malami da ake sa ran za’ayi mukabalar dashi Lamarin da ya nuna Cewa Majalisar malaman ba zata yi Zaman ba.

Dayake shedawa Jaridar Mikiya wani makusancin Sheikh Abdujabbar yace a bangaren Abduljabbar tuni ya saka hannu a takardar gayyatar da Gwamnatin Jihar kano ta aika Masa Wanda Hakan ke nuni da Cewa Abdujabbar ya aminta da Zaman Lamarin da kuma majiyar tace Mai bawa Gwamna shawara Kan harkokin addinai Ali baba Agama lafiya Yace dasu haryanzu sauran malaman da za’ayi Zaman dasu sunki aminta su saka hannu a takardar gayyatar mukabalar da Gwamnatin Jihar kano ta aika masu Amma dai anasa ran Ali baba Zai tattauna da manema labarai Kan Batun a daren Yau…

Idan baku manta ba a makwanni biyu da Suka wuce Gwamnatin jihar Kano karkashin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da dakatar da karatun Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara Sakamakon Wasu maganganu da Gwamnatin tace sun sabawa Koyarwar Addinin Muslunci Kan Annabi Muhammadu SAW Lamarin da malamin shi Kuma ya bayyana Cewa duk wani Abu da akaji ya furta to Acikin littafi ya Ciro Don Haka malamin Yace dakatar dashi da Gwamnatin tayi ba Adalci bane Hakan yasa Gwamnatin ta shirya mukabala Amma Bayan sanarwar shirya mukabalar Wasu da dama daga Cikin malaman Sunnah sun kalubalanci Al’amarin inda suke ganin yin mukabalar ba wani Abu da zai haifar face tashin hankali…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button