Labarai

Makoki: Saboda Mutane Ɗari Sunce Ga Garin ku Nan a Kwara

Spread the love

Rayuwa bata da tabbas, idan ajali yayi kira dole aje koda ba’a shirya ba.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya kaɗu sosai abisa samun labarin rasuwar aƙalla mutane 100 a jiharsa.

Lamarin ya faru ne sakamakon wani hatsarin jirgin ruwa daya faru a ƙauyen Egbu dake ƙaramar hukumar Patigi ta Kwara.

Rahotanni sun nuna cewa, jirgin na tafiya ne akan hanyar rafin “Niger River” yayin dawowa daga wani biki daga Niger zuwa Kwara.

Gwamnan jihar ya sanarda kaɗuwar sa akan lamarin, a cikin wani rahoto da babban Sakataren Yaɗa Labarai na jihar, Rafiu Ajakaye, ya saki.

Sanarwar tace:

Gwamnan yana cikin tashin hankali akan jin rahotanni na hatsarin jirgin ruwa daya lamushe mazauna garuruwan Ebu, Dzakan, Kpada, Kuchalu, da Sampi duk dake Patigi”.

Gwamnan ya kuma miƙa jaje da ta’aziyya ga mutanen yankin dama jihar baki ɗaya.

Rahoton ya tabbatar da gwamnan zai cigaba da bibiyar lamarin don ganin an ceto ɓurɓushin masu rai.

Ya kuma yabi masu mulkin gargajiya da jami’an karta-kwana abisa kawo agajin da sukayi domin ceto.

Kawo yanzu, yan sanda basu tabbatar da adadin mamatan ba, amma rahotanni na farko farko na nuna sun zarce ɗari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button