Ilimi

Makomar ilimin AREWA Bayan Cutar Korona

Spread the love

Makomar Dalibai Bayan Rabuwa Da Covid-19;

•Nazari: Arewa Students Orientation Forum.

Zuwan Annobar Coronavirus, Yayi Babbar illa ga kowanne Bangaren Rayuwar Dan Adam, Musamman a Yankunan Da Cutar Akace Ta Bulla, Ciki Harda Nigeria Dama Arewacin Nigeria.

Cutar Korona Tayiwa Bangaren ilimi Babbar asara dakuma Kawo Tsaiko Wanda Hakan ya tilasta Rufe Makarantun Nigeria Baki Daya tsawon Watanni.

Daliban kowanne Rukuni Sun Rasa Makomar Su Bayan Da Rufe Makarantun Ya Tsawaita, Koda Yake a Farkon Lamarin Wasu Jihohin Sun kirkiro Da Hanyar Koyo daga gida ta Radio Wanda Hakan beyi Tasiri ba.

•Dalibai Masu Neman Admission; Su kuwa Rukunin Dalibai dake Neman Admission a Makarantun Gaba Da Sikandire, Sun Shiga Rudani inda Dafarko akayi ta Kai komo Akan Batun Rubuta Jarrabawar Kammala Sikandire ta WAEC, NECO, NABTEB Da Nbais, inda Galibin Daliban Suna Buqatar Jarrabawar Kafin Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire.

•Dalibai Farin Ciki Har Kunne Bayan da Suka Samu Lbrn za’ayi Jarrabawar Kammala Sikandire a wancen Lokacin, saide a Yanzu za’a iya Cewa dasauran Runa a-Kaba, Domin Kuwa Jinkirin Yin Jarrabawowin Yakara Jefa Daliban Cikin Garari Na Rashin Tabbas, Domin Dayawa Daga Cikin Makarantun Gaba Da Sikandire Sun Fara Yin Rijistar Online wato POST UTME Yayinda Wasu Makarantun basa bayar da Dama ga Wanda Basu da Jarrabawar Kammala Sikandire a Hannu Suyi Rijistar.

•Daliban Direct Entry; (DE) Ga Daliban De ma Haka Abun Yake Domin Kuwa dayawa daga Cikin su, Sun Shiga Halin Rashin Tabbas a Lokacin da aka rufe Makarantun su, suna tsaka da Jarrabawar Kammala Ajin Karshe kokuma gab da Fara Jarrabawar, Hakan yasa dayawa Daga Cikin su Tunanin Makomar Su Duk Da suncika DE.

•Daliban Dake Tsaka Da Karatu; (Returning) Rukunin Daliban Dake tsaka Da Karatu Haka Suma abun Yake Domin Har Sun Kosa Da Batun yaushe Ne za’a Koma Makarantun.

•Samun Sauqi; a Yanzu za’a iya Cewa Sauqi Yafara Samuwa Domin Kuwa Jihohi Dayawa sun ayyana Ranakun Komawa Makarantu A Jihohin Su, Koda Yake galibi Banda Makarantun Gaba Da Sikandire inda Wasu Suke Hasashen sai Sabuwar Shekara.

•Mafita Ga kowanne Rukunin Dalibai; Bibiyar Al’amuran Makarantar Da Dalibi Yake Nema tare Da Yin Abunda yadace da Makarantar Ta Tsara dakuma Yin amfani Da Kungiyoyin Dalibai Dake Makarantun Dan magantuwa Da Hukumar Makarantun Kan Halin Dayake a bayyane Wanda Dalibai Suke Ciki Na Rashin Sakamakon Jarrabawar su a Hannu Kawo Yanzu.

•Ga Rukunin Dalibai Masu neman admission Both UTME Da De;

Rukunin Dalibai (Returning) kuwa Yakamata Su Maida Hankali Kan Abubuwan Rayuwar su dazai amfane su, kamar su Koyon Sana’a ko Kwarewa a Wasu bangarori Na ilimi Dakuma uwa uba Bibiyar Karatun su ta Wasu shafuka Da’ake Koyar da ko yada bangarorin su.

•Kammalawa; Hakika Cutar Korona Da’aka Yayata Tayiwa Bangaren ilimi Babbar asara Dakuma Samar Da babban gibi a, AREWA Dama Nigeria Baki Daya Wanda Hakan yasa Dole sai mun Tashi tsaye Kafin mu iya cike Wannan Gibin.

Nazari Daga Kungiyar Dalibai Ta AREWA STUDENT’S ORIENTATION FORUM
@ASOF_2020 WHATSAPP_08038485677

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button