Malam Ka watsar da Amurka Kaji Da Matsalar Kasarka: Sakon Fitaccen Mawaki Wizkid ga shugaba Buhari
Fitaccen Mawakin da aka fi sani da Wizkid ya koka da yadda SARS su ke kisan gilla, sannan Wizkid ya bukaci Buhari ya ji da wannan, ya rabu da harkar kasar Amurka
Tauraron Mawaki, Wizkid, ya yi martani game da sakon da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa Donald Trump da kuma iyalinsa.
Ayodeji Ibrahim Balogun wanda aka fi sani da Wizkid ya yi Soki shugaban kasarsa, ya ce ya fita harkar shugaban Amurkan, ya ji da Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan jama’a sun fito kafafen sadarwa na zamani su na kiran gwamnatin tarayya ta yi wani abu game da ta’adin Dakarun SARS.
Mawaka irinsu Wiz Kid, Davido, Don Jazzy su na cikin wadanda su ka huro wuta a kan a kawo karshen kisan gillar da SARS su ke yi wa Bayin Allah a Najeriya.
A dalilin haka ne Tauraron ya yi wa shugaba Buhari raddi kan maganar da ya yi a Twitter, ya ce ya kyale Donald Trump, ya yi maganin jami’an SARS.
Ya rubuta a shafinsa: Donald Trump ba matsalar ka ba ce! Dattijo! Yan Sanda/SARS su na kashe matasan Najeriya kullu Yaumin. Ka yi wani abu akan lamarin
Mawakin ya kara da cewa: Babu abin da ya hadaka da Amurka. Ka ji da kasarka”
Tauraron Mawakin mai mabiya miliyan bakwai a shafin Twitter, ya yi irin wannan kira ga gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya takawa jami’an burki. Za ku iya tunawa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya na cikin wadanda su ka yi maza su ka yi magana bayan jin cewa Donald Trump ya kamu da COVID-19.
Shugaba Buhari ya bi sahun shugabannin kasashen duniya, ya jajantawa Trump da mai dakinsa Melania. Daga Comr Haidar Hasheem Kano