Malam Pantami ya kaima jihohin arewa maso gabas cigaba
Sheikh dr ali isa pantami Ministan ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa
Alhamdu lil Laah! Daga cikin hanyoyin da na kai kukan su, zuwa ga abokanen aiki na, wato Ministocin Ayyuka domin Jama’ar Jihar Gombe, wanda dokokin Najeriya su ka nuna nake wakiltansu. Akwai tafiyar hawainiya na aikin hanyar Gombe zuwa Yola. Wannan hanyar an bada aikin ta tun 2017, amma aiki baya tafiya kwata-kwata.
Bayan ziyarori da yawa da na kai zuwa ga Ministocin ayyuka, bincike ya tabbatar cewa akwai matsalolin (Black Cotton Soil, and the replacement of a single span bridge, da makaman tansu, musamman tsakanin Cham da Numan).
Wadannan matsaloli da na bayyana yasa aikin baya tafiya, domin kudin aikin yayi kadan, kuma ba zai kammala aikin ba. Dalilin roko da muka kai, a yau zaman da aka yi na Federal Executive Council, wanda shugaban kasa ya jagoranta, an kara kudin aikin Tsakanin Cham na Jihar Gombe zuwa Numan da ke Jihar Adamawa. Kudin da aka kara, don kammala aiki mai nagarta, shine Naira Biliyan Bakwai, da miliyan Dari Shida da bakwai, da dubu dari hudu da hamsin, da dari bakwai da arba’in da tara, da kobo ashirin da hudu. (N7, 607,450,749.24).
Don haka a yanzu a cikin hanyoyi hudu da muka isar da damuwa akansu, uku sun samu shiga, saura daya, wanda itama ta Jiha ce, amma duk da haka muna kokarin samun tallafin gwamnatin tarayya don tallafawa Jihar mu ta Gombe in sha Allah.
Allah Ya sa a kammala aiki mai nagarta, kuma Ya sanya shi mai anfani ga Al’Ummah. Ameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum.
Isa Ali Ibrahim Pantami.