Labarai

Malamai sun bamu shawara sunce karmu aminta ayi mukabula da Sheikh AbdulJabbar ~Inji Ganduje

Gwamna Dr Abdullahi Ganduje Yace dakatar da Sheikh AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara : “Daukar Mataki Da Mu Ka Yi Yanzu Mu Ka Fara,” In Ji Gwamna Ganduje

  • Malamai sun ce ba bukatar muqabala da wanda ya yi batunci ga janibin Annabi Muhammad, Sallallahu Alaihi Wasallam
  • Sarkin Musulmi da Wazirin Katsina sun aiko da sakon jinjina ga Gwamna Ganduje

Matakin da gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kan hana karatuttukan AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara, a Masallacinsa da ragowar wurare, Gwamna Ganduje ya ce “Wannan matakin yanzu ma mu ka fara dauka. Akwai abubuwan da za su biyo baya.”

A wani taro na musamman da Gwamnan ya kira dukkan bangarori na Malamai da kuma Limaman Masallatan Juma’a, wanda a ka yi a dakin taro na Africa House, da ke gidan gwamnati, yau Alhamis, ya ce “Da can mu na ta jin abubuwan da a ke fada sai mu ka ce a kawo mana hujja kan hakan. Mu na samun hujja sai mu ka dauki mataki kamar yadda a ka fara gani.”

Ya kara da cewa “Wannan hobbasa, ba ta gwamnati ba ce ita kadai. Ta mu ce gaba daya. Babban abin haushin ma shine, bayan karuwar faruwar irin wannan abu, sai ya zamana ma cewar abin ya na ma kara zurfi. Idan a ka yi la’akari da yadda wannan abin ya faru.”

Gwamnan ya shawarci Limaman Juma’a da cewar ya kamata Hudubobinsu na Sallar Juma’a gobe su mayar da hankali kan wannan magana da a ke ciki.

“Ya kamata a kara nunawa al’umma munin wannan babban al’amari. Da kuma neman karin addu’o’i daga al’umma kan cewa Allah Ya sa wadannan matakan da mu ke dauka su zame mana dalilin Tsira gobe Kiyama.”

Sa’annan ya kara da cewa zai ci gaba da zama da Malaman saboda tuntubarsu kan yadda abin zai dinga tafiya. Ya kuma kara neman goyon bayan al’umma da ci gaba da yi wa jihar ta Kano addu’o’i kamar yadda a ka saba yi.

Daga cikin malaman da su ka tofa albarkacin bakinsu, sun hada da dan uwan AbdulJabbar din na jini, wato Alkali Mustapha Sheikh Nasiru Kabara, wanda ya bayar da shawarar cewar “Wannan magana ba wai magana ce ta muqabala ba. Wato ba maganar wai sai an zauna da shi ba ne. Ba abinda ya dace da shi illa a kai shi Kotun Musulunci.”

Shi ma Limamin Masallacin Al-Furqan, Dr Bashir Aliyu Umar, cewa ya yi “Wannan ai ko kadan ba magana ce ta a zauna da wannan mutumin a yi Muqabala ba ne. Ai a irin wannan mas’ala a Musulunci ba a bukatar wai a ji dalilan mutum na yin abinda ya yi.”

Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, shugaban Izalatul Bid’ah Wa’ikamatussunnah na Kano, kuma Shugaban Hukumar Alhazai Ta Jihar Kano, cewa ya yi “Ba maganar wata mahawara da wanda ya zagi Annabin Tsira Sallallahu Alaihi Wasallam.”

Shi ma Shehi Shehi Maihula da Sayyadi Bashir Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebari da Malamai da su ka yi magana a wajen, dukkansu sun hadu kan cewa ba bukatar zaman yin mahawara da duk mutumin da ya yi irin wadancan maganganu na batunci.

Sa’annan a jawabinsa na bude taro da takaitaccen bayani, Kwamishinan Harkokin Addini, Dr Muhammad Tahar Adam, ya bayyana irin sakonnin da su ke samu daga jama’a daban daban na yabawa da wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka.

Ya ce “Maigirma Gwamna, mu na ta samun sakonni daga gungun al’umma daban daban na goyon bayan wannan mataki da a ka fara dauka. Daga baya bayan nan mun samu sakon gaisuwa da jinjina daga Sarkin Musulmi da kuma Wazirin Katsina.”

Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Alhamis, 4 ha Watan Fabrairu, 2021
[email protected]
[email protected]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button