Malaman Addini ne suke hura wutar rikicin jahar Kaduna – A cewar Nasir El- rufa’i
Gwamnan jihar kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya zargi wasu malaman addini da cewa sune ke haifar da tashe tashen hankula a jihar.
El-Rufai wanda ya yi magana a lokacin da Primate of the Anglican Church of Nigeria, Mafi Reverend Henry Ndukuba, ya jagoranci wata tawaga a wata ziyarar girmamawa a fadar gwabnatin jahar Kaduna, ya ce “manyan masu tayar da wannan rikici malamai ne don basa wa’azi akan mihimmancin zaman lafiya ko inganta rayuwar dan adam ba Maimakon haka suna amfani da malantar su don samu girma da matsayi da rarraba kan Al’umma Wanda ke haifar da rikici
Tun da farko Reverend Ndukuba ya ce “Na yi imanin cewa idan Kirista za su tsaya kan abin da suka yi imani kuma musulmai za su tsaya kan abin da suka yi imani kuma kowannensu ya yi abin da ya kamata a yi la’akari da dan uwansa da‘ yar uwarsa da makwabta na yi imani cewa muna da duk abin da ake bukata na wanzuwar Zaman lafiya .Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano