Malami Ya shiryawa magu makirci ta hanyar Abdulrashed maina a kokarinsa na tona masa asiri
Kwamitin binciken da Shugaban Muhamamdu Buhari ya kafa don bincikar ayyukan Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, Ibrahim Magu, an ba shi sabon makonni shida don ci gaba da aikin Shugaban kwamitin, Justice Ayo Salami (mai ritaya) , ya nemi yin tafiya zuwa Burtaniya don “binciko” shari’ar tsohuwar Ministar albarkatun Petroluem, Diezani Alison-Madueke, wacce aka zarga da karkatar da kudade ta wata hanyar. A wani yunkuri na fallasa Magu, kwamitin na shirin kawo tsohon Shugaban rusasshiyar kungiyar gyara Fansho Abdulrasheed Maina, domin ya bayar da shaida kan tsohon mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC. An tattaro cewa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, yana karfafa wa Maina gwiwa Kan cewa ya rubuta koke yana neman a sake duba karar tasa a kokarin ministan na shirya makirci ga Magu ya cika.