Man United Na Son Dauko ‘Yan Wasa Uku, Barcelona Na Zawarcin Thiago
Makomar Sancho, Bale, Telles, Brewster, Thiago, Mendy, Kante, Tarkowski
Manchester United na fatan daukar karin ‘yan wasa uku kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan kwallo ta bazara kuma dauko dan wasan Borussia Dortmunddan kasar Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, shi ne babban abin da ta sanya a gaba. (Manchester Evening News)
Damar da kocin Real Madrid Zinedine Zidane yake da ita ta yin garambawul ga kungiyar ta dogara ne kanyiwuwar Manchester United ta daukar mataki a kan dan wasan Wales mai shekara 31 Gareth Bale. (Marca – in Spanish)
Wakilan dan wasan Porto da Brazil mai shekara 27 Alex Telles sun tafi Manchester domin tattaunawa da United. (A Bola, via Metro)
Manchester City za ta dauko dan wasan Sevilla dan kasar Brazil Diego Carlos, mai shekara 27, da dan wasan Atletico Madrid dan kasar Uruguay Jose Gimenez, mai shekara 25, a madadin dan wasan Napoli dan kasar Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29. (Sport – in Spanish)
Aston Villa na son sayo dan kasar Ingila da ke murza leda a Liverpool Rhian Brewster mai shekara 20 a kan £20m. (Sun)
Kungiyoyin Firimiya sun yi amannar cewa za a bar Brewster ya fice daga Liverpool a lokacin musayar ‘yan kwallo, a yayin da Sheffield United da kuma Crystal Palace suke zawarcinsa. (Telegraph – subscription required)
Barcelona na sha’awar dan wasan Bayern Munich dan kasar Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29 – wanda Liverpool ke son daukowa. (Bild – in German)
Chelsea na fatan kammala sayen golan Rennes dan kasar Senegal Edouard Mendy, mai shekara 28. (Telegraph)
Kazalika Chelsea na fatan kulla yarjejeniya da Rennes bayan ta mika mata £20m da kudin talla don karbo Mendy. (Mail)
Kocin Inter Milan Antonio Conte yana fatan dauko dan wasan Chelsea dan kasar Faransa N’Golo Kante, mai shekara 29, ko da yake farashinsa zai kai £60m. (Calciomercato – in Italian)
Mai yiwuwa Arsenal ta samu damar dauko dan wasan Atletico Madrid dan kasar Ghana Thomas Partey, mai shekara 27, a yayin da Madrid ke bukatar karin kudi domin dauko dan wasan Espanyol mai shekara 23 dan kasar Sufaniya Marc Roca. (Marca, via Mirror)
Daga Amir Sufi