Labarai
Manoman yankin Inyamurai sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta biyasu diyyar biliyan 9 na amfanin gonakinsu da Fulani Makiyaya suka lalata musu.
Kungiyar manoma a karkashin manoman yankin Inyamurai ta nemi gwamnatin tarayya da ta basu diyyar Naira Biliyan 9 saboda Asarar amfanin gonar da Fulani Makiyaya suka yi musu.
Kungiyar ta ce sakacin gwamnatin tarayya ne yasa har manoman suka yi mata waccan barna dan haka ne ma take son gwamnatin ta mayar mata da asarar da ta tafka.
Shugaban kungiyar, Paul Achalla ya ce gwamnatin tarayya Fulani kadai take biya diyya amma su ba ta biyansu, inda yace suna kira ga kungiyar gwamnonin yankin da ta Ohanaeze su taimaka musu su wa gwamnatin tarayya magana ta biyasu diyya.