Lafiya
Martanin El-Rufa’i Ga Gwamnatin Tarayya Akan Janye Dokar Zaman Gida.

Daga Kabiru Ado Muhd
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i Ya Mayarwa Da Gwamnatin Tarayya Martani Akan Umarnin Da Ta Bayar Na Bari Jama’a Suci Gaba Da Mu’alolinsu Na Yau Da Kullum.
Gwamna El-Rufa’i Ya Ce
“Jihar Kaduna Ba Abuja Bace, Don Haka Ni Ke Da Iko Da Jihata. Maganar Najanye Doka Baki Daya Ba Zan Janye Ba A Halin Yanzu.”
Sai Dai Kuma Mutane Da Dama Na Ganin Bai Kamata Gwamnan Yaki Sassauta Dokar Ba, Duba Da Jihar Kaduna Bata Daga Cikin Jihohi Masu Yawan Adadin Masu Dauke Da Wannan Cuta Ta Covid 19.
Inda Wasu Kuma Suke Ganin Gwamna Yayi Daidai, Harma Suke Cewa Yana Daukar Wadannan Matakan Ne Domin Kare Lafiyar Al’ummar Jiharsa.