Wasanni
Masana’antar Bollywood Ta Sake Rashin Wani Fitaccen Jarumi.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Masana’antar ta Bollywood sun shiga jaje da alhini na sake rashin Jarumi dasukayi Rishi Kapoor, wannan yafarune biyo bayan rasuwar Irfan Khan wanda shima shahararrene a Indiya da fadin duniyar Wasan Kwaikwayo.
Jarumin ya rasune yau Alhamis bayan yayi fama da cutar Daji wacce akafi sani da Cancer na tsawon lokaci.
Rishi Kapoor ya rasu yanada shekara 67 a duniya yayin da ya shafe dogon lokaci yana shirya wasannin kwaikwayo a masana’antar ta Bollywood.