Masarautar Zazzau Ta Dakatar Da Marafan Yamman Zazzau Bisa Laifin Yiwa Wani Mutum Bulala A Zariya
Majalisar Masarautar Zazzau ta jihar Kaduna ta dakatar da wani mai rike da sarautar gargajiya a masarautar, Alhaji Mustapha Adamu, bisa laifin yi wa wani mutum bulala a karamar hukumar Zariya da ke jihar.
Jami’in yada labarai da sadarwa na Masarautar Zazzau Abdullahi Aliyu ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata.
Ya ce dakatarwar da aka yi wa Adamu wanda ke rike da sarautar Marafan Yamman Zazzau ya biyo bayan kin bin doka da oda ne ta hanyar yi wa wani Yusuf Yahaya (SABO) dan Unguwan Magajiya Zariya bulala 60.
A cewar Aliyu, dakatarwar ba ta fara kuma nan take.
Sanarwar ta yi gargadin cewa Masarautar Zazzau ba za ta amince da duk wani abu da ya saba doka da oda daga duk wani mai rike da sarautar gargajiya a cikin al’umma ba.
Ta kuma shawarci masu rike da mukaman gargajiya da su rika mika kararrakin da ke gabansu ga hukumomin da aka kafa domin yanke hukunci mai kyau maimakon daukar doka a hannunsu.
Mustapha Adamu ya nuna rashin jin dadinsa kan matakin gaggawar da Masarautar Zazzau ta dauka a kansa ba tare da yi masa adalci ba. Ya kuma zargi wasu ‘yan majalisar masarautun da rura wutar lamarin.