Masha Allah: Saukar Alkur’anin da ‘yan jihar Borno sukai akan ta’addancin boko haram ya fara haifar da labari mai dadin ji.
‘Yan kungiyar boko haram a jihar Borno sun yi kashe kashe a junan su akan hanyar su ta kawo hari kauyen diffa da misalin karfe hudu Na yammacin yau litinin.
Rigimar data faru ijunan su ta faru ne sanadiyar sabanin ra’ayi da suka samu a tsakanin su, wani tsagin daga cikin su sun nemi da kada akai harin sai cikin dare, wani tsagin kuma sukace a’a tunda an riga an taho kawai a aiwatar.
Hakan tasa zargin munafuntar juna ya jawo rigama ta balle a tsakanin su, Wanda yanzu maganar da ake sama da ‘yan boko haram dari biyu da wani Abu sun mutu har lahira sakamakon rikicin da ya barke ijunan su.
Mutanen kauyen diffa ne da suka rika jiyo harbe harbe ya yi yawa suka bazamo daga cikin kauyen don tsira, daga bisani Jami’an tsaro suka ankara suka nufi wajen, bayan sun tunkari wajen sai ‘yan boko haram din suka tarwatse suka bar gawarwarkin da suka kashe na ‘yan’uwansu a wajen.
Jami’an tsaro sun sami tabbacin haka ne ta sanadin wadanda suka jikkata bayan sun tattara su.
Daga Kabiru Ado Muhd