Tsaro

Masu Garkuwa da Mutane sun kashe wani Manomi duk da sun karɓi kuɗin Fansa N1.65m daga Iyalansa.

Spread the love

Wani manomi a Ibadan, Oluwole Agboola, wanda aka sace a ranar 28 ga Disamba, 2020, an tsinci gawarsa a ranar Talata bayan wadanda suka sace shi sun karbi kudin fansa na Naira miliyan 1.65.

An sace Agboola ne a gonarsa da ke yankin Abaodo a kauyen Olukitibi a karamar hukumar Akinyele da ke jihar, wasu ‘yan bindiga dadi shida ne suka saceshi.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito, masu garkuwan sun amshi kudin fansa na naira miliyan 1.65 daga dangin wanda suka sacen kuma kawo yanzu sun kashe shi.

Wani dan uwan ​​mamacin, Olakunle Agboola, ya tabbatar da kisan manomin ga manema labarai a ranar Talata.

Ya ce ‘yan bindigan sun kashe dan uwansa kwanaki 10 bayan sun karbi kudin fansar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button