Rahotanni

Masu Garkuwa Da Mutane Sunje Har Gidanshi Dake Garki Jigawa Sun Tafi Dashi…

Spread the love

A daren jiya masu garkuwa da jama’a suka je har gida suka yi awon-gaba da Alhaji Surajo Body a garin Garki jihar Jigawa.

Haƙiƙa wannan bawan Allah mutum ne da ya yi suna sannan ya ciri tuta ta fuskar tallafawa al’umma musamman masu ƙaramin ƙarfi, ko a hanya kuka haɗu dashi idan rabonka ya rantse sai ya yi maka kyautar da sai ka sha mamaki.

Mutane da yawa sunyi ittifaƙin duk cikin kwaryar garin Garki babu mutum mai taimako sama dashi.

Dan haka, muke roƙon ƴan uwa na kusa dana nesa dasu saka wannan bawan Allah a cikin addu’o’insu domin Allah ya kuɓutar dashi cikin Salama da kwanciyar hankali.

Daga Mutawakkil Gambo Doko.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button