Rahotanni

Masu Kananun Albashi Sun Samu Tallafi A Jihar Kaduna.

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

A karo Na Biyu Gwamnatin Jihar Kaduna Tare da Hadin Gwuiwar Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufa’i, Sun Kaddamar Da Rabon Tallafi a Jihar.

Wadanda Suka Amfana Da Tallafin Dai Sune Ma’aikatan Jihar Masu Daukar Kananan Albashi, da kuma Sauran Al’umma Masu Karamin Karfi.

A Jawabin Da Sakataren Gwamnatin Jihar Ta Kaduna, Balarabe Abbas Lawal, ya Fitar a Ranar Juma’a, ya Bayyana Cewar An Raba kayan Rage Radadin ne Ga Mabukata Kafin Ranar Sallah, Domin Suma Su Gudanar Da Bukukuwan Sallah a Cikin Natsuwa Tareda Kwanciyar Hankali.

Balarabe ya kara Da Cewar Za’a Raba Kayayyakin Abincinne a Kananan Hukumomi 14, Yayinda Magidanta 32,000 ne Zasu Amfana Da Kayayyakin Tallafin,

Malam Balarabe ya kara Da Cewar wasu daga Cikin Kayayyakin Da Za’a Raba Sun Hadarda Shinkafa, Wake, Semovita, Masara, Flour, Garri, Taliyar Spaghetti, dakuma Man Girki, Wanda Zuwa Yanzu Kayayyakin sun isa Zuwa Kananan Hukumomin Da Za’a Rabasu

Malam Balarabe Wanda Shugaba ne a Kwamitin Ragewa Al’umma Radadi Bisa Wannan Annoba Ta Covid – 19 a Jihar Ta Kaduna, Ya Bayyana Cewar Hakika Dukkannin Mutanen Da Za’a baiwa Wannan Tallafin sun Cancanta, Domin kuwa Dukkannin Su Mutane ne Masu Kananun Albashi, da kuma Sauran Talakawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button