Masu Zanga Zangar Juyin Juyahali Sun Zargi Jami’an Tsaro da Cin Zarafinsu…
Kakakin Kungiyar Nan Mai fafutuka tabbatar da Dimokuradiyya da kare Hakkin bil adama ta Najeriya, Mr. Agada Abu Theophilus ya Zargi Jami’an Tsaron Najeriya da Take Hakkin masu zanga zangar a Abuja, Legas da Sauran Jihohi.
Mr. Theophilus “Yace Masu zanga zangar suna gudanar da zanga zangar ne kan Rashin Iya Mulki Na Shugaban kasa Buhari.
Sannan yace yan kasar suna da damar yi zanga zangar a duk lokacin da Aka shiga Irin wannan Mummunan Yanayin Na Rashin tsaro da Koma baya wajen Tattalin arziki a kasar nan.
Theophilus ya zargi Jami’an Tsaron Inda yace basu iya Aikin suba sannan Suna cin zarafi da Tsangwamar yan Kasar a duk lokacinda Yan kasar suka tashi Neman `Yan cinsu Inji Shi.
Idan Baku manta Ba a Yau Larabane dai Kungiyoyi suka gudanar da zanga zaga kan Rashin Iya shugabancin Shugaban Kasa Buhari, duba da Yadda Rashin Tsaro, Tabarbarewar Tattalin Arziki da koma baya ta kowanne Fanni ya Addabi Kasar Nan-Inji masu zanga zangar.
An gudanar da zanga zangar ne a Jihohin;- Abuja, Legas. Neja, Ondo da Sauransu.
Ahmed T. Adam Bagas